Hebrews 4

1Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah. 2Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba.

3Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, “Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba.” Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya. 4Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, “Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa.” 5Ya sake cewa, “Baza su taba shiga hutu na ba.”

6Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra’ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya, 7Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, “Yau.” Ya sa wannan rana sa’adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, “Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”

8Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba. 9Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah. 10Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa. 11Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi.

12Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta. 13Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi.

14Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi. 15Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba’a same shi da zunubi ba. Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

16

Copyright information for HauULB